Rasha ta tsunduma cikin yakin Siriya | Labarai | DW | 30.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha ta tsunduma cikin yakin Siriya

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya ce mayakan saman kasarsa za su rinka taimakawa dakarun kasar Siriya a yakin da suke da 'yan kungiyar ta'addaan IS.

Shugaba Vladimir Putin na Rasha

Shugaba Vladimir Putin na Rasha

Kamfanonin dillancin labaran kasar ta Rasha ne suka ruwaito cewa Putin ya bayyana hakan ne a wannan Laraba, inda ya ce Rasha ba za ta sake zuba idanu ta zamo 'yar kallo a rikicin na Siriya ba, za ta taimakawa sojojin Shugaba Bashar al- Assad. Putin ya kara da cewa ya na tsammanin Assad zai zauna da 'yan adawar kasar domin tattauna makomar kasar Siriyan a siyasance. Tun da fari dai da sanyin safiyar wannan Larabar majalisar dattawan kasar ta Rasha ta amince da bukatar Putin na tura dakarun kasarsa zuwa Siriya.