1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta musanta zargin karbe iko a Ukraine

January 23, 2022

Rasha ta sa kafa ta shure zargin da Birtaniya ta yi mata na cewar tana tuntubar wasu tsoffin 'yan siyasa a Ukraine a kokarinta na kawar da gwamnati mai ci yazu a Ukraine.

https://p.dw.com/p/45yA5
Fahnen UK Ruslannd
Hoto: daniel0Z/Zoonar/picture alliance

Da yammacin ranar Asabar ne Birtaniya ta fidda wata sanarwar da ke zargin Rasha da kokarin kafa gwamnati a Ukraine din.

Ma'aikatar kula da harkokin kasashen ketaren Birtaniyar dai ba ta bayar da wata hujja da ke tabbatar da zargin nata ba.

A baya-bayan nan dai dangantaka ta yi tsami a tsakanin Rasha da kasashen yamma, saboda girke dakaru sama da dubu 100 da Rasha ta yi a gabashin Ukraine.

Sai dai Rashar ta karyata zargin da akasashen ke yi mata na kai wa Ukraine mamaya.