Rasha ta kwace ikon wasu kauyuka a gabashin Ukraine
November 23, 2025
Dakarun Kyiv na kokarin ganin sun rike iko da yankunan gabashin Ukraine, sai dai sojojin Rasha na ci gaba da samun galaba a kai. Kara zafafa kai hare-haren na Rasha na zuwa ne yayin da Amurka da Kyiv da kuma wakilan kasashen yammacin Turai ke shirin ganawa a Geneva, domin tattauna kwarya-kwaryar daftarin shirin samar da zaman lafiya a Ukraine.
Karin bayani: Rasha ta kwace garuruwan Ukraine a wani sabon farmaki
Shugaba Trump na Amurka ya bai wa Ukraine wa'adin ranar 27 ga watan Nuwambar 2025 domin ta yi nazari kan shirin da ya gabatar, na kawo karshen yakin da aka kwashe kusan shekaru hudu ana gwabzawa, sai dai gwamnatin Kyiv na neman sauya wasu daga cikin bukatun da suka fifita bukatun Rasha. Bukatun sun hada da bai wa Rasha iko da wasu yankunan Ukraine, da rage yawan dakarunta da ma yin watsi da burinta na son shiga kungiyar kawancen tsaro ta NATO.