1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Rasha ta cafke mutane 11 da ke da hannu a hari

March 23, 2024

'Yan bindiga da suka yi shigar burtu sun kashe mutane kimanin 143 a wajen wani biki da ke birnin Moscow na kasar Rasha, a hari da IS ta dauki nauyin kaiwa. Amma Rasha ta cafke mutane 11 da 'yan bindiga 4 da ake zargi.

https://p.dw.com/p/4e39I
Jami'an rasha na ci gaba da bincike don gano wadanda ke da hannu a harin Moscow
Jami'an rasha na ci gaba da bincike don gano wadanda ke da hannu a harin MoscowHoto: picture alliance/AP

Hukumar leken asirin kasar ta FSB ta sanar da cewa ta cafke mutum hudu da ke da hannu a harin a kan hanyarsu ta zuwa kasar Ukraine, inda suka dawo dasu Moscow domin ci gaba da gudanar da bincike.  Shi ma wani dan majalisar dokokin Rasha Andrei Kartapolov ya ce idan har ta tabbata Ukraine ce ta kitsa harin, to akwai bukatar Rasha ta zafafa hare-haren da take kai wa Ukraine. Amma Ukraine ta nesanta kanta daga harin gidan gala a birnin Moscow. Wannan ne farmaki mafi muni da aka kai Rasha tun daga 2004, bayan wani hari da aka kaiwa 'yan makaranta tare da bude wuta ga fararen hula a arewacin babban birnin kasar.

Karin bayani: Shugaba Putin na Rasha ya ce akwai yiwuwar yakin duniya na uku

Wani Sojan Rasha a kusa da inda 'yan bindiga suka kai hari a Crocus City Hall dake wajen birnin Moscow.
Wani Sojan Rasha a kusa da inda 'yan bindiga suka kai hari a Crocus City Hall da ke wajen birnin Moscow.Hoto: AP Photo/picture alliance

Wasu hotunan bidiyo da aka wallafa sun nuna yadda 'yan bindigar suka shiga cikin dandalin da ake gudanar da rawar, wanda daga bisani suka bude wuta akan mai uwa-da-wabi, bayan sun datse hanyar fita daga dandalin. Kazalika wasu hotunan bidiyo sun nuna tarin mutane a kwance cikin jini da suka da ke da sauran numfashi ke kokarin yunkurawa domin tsira daga farmakin.

Karin bayani: Matsayin Rasha a Gabas ta Tsakiya

Tuni dai shugaban hafsan tsaron Rasha Alexander Bortnikov da shugaban hukumar leken asirin kasar suka kaddamar da bincike kan musabbabin kai harin tare da sanar da shugaban kasar Vladimir Putin halin da ake ciki, acewar wata sanarwa daga fadar kremlin. Kazalika an tsaurara tsaro a ciki da wajen babban birnin tare da rufe dukkan iyakokin kasar ta sama ta kasa domin daukar matakan gaggawa na shawo kan lamarin.

 

Shugabannin kasashen duniya sun yi  amfani da kakkausar murya wajen yin Allah wadai da harin da kungiyar IS ta kai a birnin Moscow. Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ta bakin mai magana da yawunsa Farhan Haq ya bayyana harin a matsayin ta’addanci da ke ci gaba da yaduwa a duniya tare da mika ta’aziyya ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su da kuma gwamnatin Rasha.

Karin bayani: Zaben Rasha 2024: Me ya sa Putin ya damu da yin zabe?

'Yan Rasha da shugabannin duniya na nuna alhani kan harin Moscow
'Yan Rasha da shugabannin duniya na nuna alhani kan harin MoscowHoto: picture alliance/dpa/TASS

A nata bangaren, fadar mulkki ta White House ta Amurka ta  aike da sakon ta'aziyya ga kasar Rasha, inda ta ce hotunan wannan lamari na da ban tsoro da wuyan kallo. Shi ku wa shugaban kasar Sin Xi Jinping, wanda ke dasawa da kasar Rasha, ya mika sakon ta'aziyyarsa tare da jaddada cewa, kasar Sin na adawa da duk wani nau'in ta'addanci. Su ma shugabannin kasashen Jamus da Japan da Italiya da Belarus da Mexico da Venezuela sun mika sakon ta'aziyyarsu.

A nata bangaren, kungiyar tarayyar turai ta bayyana kaduwarta dangane da harin na Moscow tare da bayyana cewa kungiyar na goyon bayan wadanda bala'in ya rutsa da su.