1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTarayyar Rasha

Putin ya yi jinjina ga Prigozhin

August 24, 2023

Shugaba Putin ya jinjina wa shugaban kamfanin Wagner Yevgeny Prigozhin kan gudunmowar ya bai wa Rasha a Ukraine tare da yin alkawarin gudanar da bincike kan musabbabin hadarin jirgin saman da ya yi ajalinsa.

https://p.dw.com/p/4VY9x
Kombo Prigohzin Putin
Hoto: picture alliance

A lokacin da yake mika sakon ta'aziyya ga iyalai da kuma makusantan wadanda hadarin jirgin saman ya ritsa da su, shugaba Vladimir Putin ya ce: ''Yevgeny Prigozhin mutum ne da rayuwarsa ta kasasnce cike da kalubale, sannan ya aikata kura'kurai masu girma a lokacin da yake raye, amma kuma ya samu sakamakon da ya kamata ya girba gorgodon abin da ya shuka''.

Karin bayani:Wagner: Prigozhin ya "mutu" a hadarin jirgi

Kazalika Mista Putin ya ce sauran mutanen da hadarin ya ritsa da su cikin har da na hannun daman Prigozhin da ake kira Dmitri Outkine da kuma karin wasu jigajigai a kamfanin sojojin haya na Wagner mutane ne da suka taka rawa a game manufofin Rasha kan Ukraine musanman matakin yaki da aka fara yau da shekara guda da rabi.

Karin bayani: Rasha: Ko mayakan Wagner na shirin kwace mulki?

Mutuwar ta shugaban Wagner da mukarrabansa ta buda babin mahawara a duniya tare da dasa ayar tambaya kan cewa ko Putin ya dau fansa ne kan yunkurin tawaye da Prigozhin ya yi masa watanni biyu da suka gabata.