1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha na tsananta hare-hare a Ukraine

March 23, 2023

Rasha ta ci gaba da tsananta hare-haren makamai masu linzami da na jirage marasa matuka a kan Ukraine, hare-haren da suka yi sanadiyyar mutuwar dalibai da ma wasu fararen hula.

https://p.dw.com/p/4P6Rj
Hoto: Sergey Shestak/AFP

Wannan dai wani kakkausar martani ne a daidai lokacin da ake kokarin nemo matakan diflomasiyya da nufin kawo zaman lafiya a yakin na Ukraine da yanzu ya kai watanni 13 na gwabzawa.

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy, ya bayyana takaicin yadda hare-haren ke sauka kan gidajen marasa karfi, yana cewa Rasha na bude wuta kan mutane masu rauni irin kananan yara.

Hare-haren dai na fadawa ne a kan rukunan gidaje da ke a kudancin birnin Zaporizhzhia.

A wasu hare-haren kuwa, dakarun Ukraine sun yi nasarar kakkabo jiragen Rasha marasa matuka 16 daga 21 da ta harba a kusa da birnin Rzhyshchiv da ke kudancin kasar.