Rasha na son kara karfafa alakarta da Iran
October 20, 2025
Fadar Kremli ta ce gwamnatin Moscow da man na da alaka mai karfi da gwamnatin Tehran kana ta yi Allah wadai da munannan hare-haren da Amurka da kuma Isra'ila suka kai wa Iran a cikin wannan shekarar. Kakakin Kremli, Dmitry Peskov ya soki kasashen Turai da matsa lamba kan Iran a lokacin tattauna wa kan shirinta na makamin nukiliya, inda ya bayyana lamarin a matsayin mai wuyar sha'ani.
Karin bayani:Shugaban Rasha zai gana da na Iran
Ana sa ran tawaga ta musamman ta shugaba Rasha ta gana da shugaban hukumar koli ta tsaron Iran Ali Larijani. Ganawar na zuwa ne kasa da mako guda da Larijani ya gana da Shugaba Vladmir Putin, domin ya mika masa sakon jagoran juyin juya halin Musulumci na Iran, Ayatollah Ali Khamenei.
Ko a watan Janairun 2025, Shugaba Putin da takwaransa na Iran, Masoud Pezeshkian sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu. Rasha ta ce tana siyar wa da Iran kayan soji ta hanyar da ta dace, yayin da Iran ke samar mata da jirage marasa matuka da take amfani da su a yakin Ukraine.