1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kara takunkumi kan Iran

Suleiman Babayo ATB
April 17, 2024

Kungiyar Tarayyar Turai ta duba hanyoyin kara hukunta kasar Iran da fadada takunkumin karya tattali saboda martanin makamai da ta jefa wa Isra'ila da aka dakile, sannan yadda kasar take ci gaba da bai wa Rasha makamai.

https://p.dw.com/p/4ery9
Sojan Isra'ila kusa da makamun Iran da ya fadi
Sojan Isra'ila kusa da makamun Iran da ya fadiHoto: Tsafrir Abayov/AP/picture alliance

Babban jami'in kula da manufofin kungiyar Tarayyar Turai, Josep Borrell ya bayyana cewa kungiyar ta fara duba hanyoyin fadada takunkumin karya tattalin arziki kan Iran bayan matakin mahukuntan birnin Tehran na kaddamar da farmaki a karshen mako kan Isra'ila. Borrell ya bayyana haka lokacin taron ministocin harkokin wajen kungiyar ta kafar Intanet da aka gudanar a wannan Talata da ta gabata.

Kungiyar ta Tarayyar Turai za ta karfafa matakin takunkumi saboda yadda Iran kuma take ci gaba da bai wa Rasha makamai tun bayan kutsen da Rasha ta kaddamar kan Ukraine.

Shugabannin kasashen na kungiyar Tarayyar Turai lokacin taron da suke shirin gudanarwa za su duba gaba daya yanayin da ake ciki na rikice-rikice a yankin Gabas ta Tsakiya.