Rasha: Muna tare da Iran kan nukiliya | Labarai | DW | 13.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha: Muna tare da Iran kan nukiliya

Gwamnatin kasar Rasha ta ce tana nan kan bakarta dangane da matsayin da kasashe suka cimma na yarjejeniyar makamin nukiliyar kasar Iran.

Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov shi ne ya bayyana cewa ya ce kasarsa na nan daram kan yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran, a dai dai lokacin da shugaba Donald Trump na Amirka ke cewa hakan ya saba da ra'ayin Amirka.

Wata sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta fitar, ta ce Mr. Lavrov ya shaida wa takawaransa na Iran Mohammad Javad Sharif cikakken goyon bayansu ga yarjejeniyar, wadda kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya riga ya amince da shi. Manyan jami'an biyu dai sun tattauna ne ta wayar tarho a cewar sanarwar.