1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jirgi marar matuki ya fada kan wani gini a Rasha

March 2, 2024

Rahotannin daga St Petersburg na Rasha sun yi nuni da cewa an kwashe mutane kimanin 100 daga wani ginin bene mai hawa biyar bayan da wani jirgi marar matuki ya fadawa ginin.

https://p.dw.com/p/4d6Y9
Jirgi maras matuki ya fada kan wani gini a St Petersburg
Jirgi maras matuki ya fada kan wani gini a St PetersburgHoto: Darya Ivanova/picture alliance/dpa/TASS

Gwamnan jihar, Alexander Beglov ya ce an duk da ginin ya lalace, an auna arziki kasancewar ba a samu asarar rayuka ba. Gwamnan bai yi karin bayani kan yanayin hatsarin ba da kuma musababbinsa, sai dai mazauna ginin na cewa sun ji karar abun fashewa kafin gobara ta tashi.

Kafafen yada labaran Rasha sun ce, ta yiwu jirgin mara matuki na Ukraine ne da aka harba zuwa wani tashar mai ya fadawa ginin. Sai dai ma'aikatar tsaron Ukraine ba ta ce uffan ba dangane da lamarin.