1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Ukraine ta kai hari kan jirgin Rasha a Bahar Aswad

December 26, 2023

Ma'aikatar tsaron Rasha ta tabbatar da cewa Ukraine ta kai kari kan wani jirgin ruwanta na yaki a kusa da gabar kogin Bahar Aswad

https://p.dw.com/p/4ab46
Hoto: Sergei Malgavko/TASS via picture alliance

Ma'aikatar tsaron Rasha ta tabbatar da cewa Ukraine ta kai hari kan wani jirgin ruwanta na yaki a kusa da gabar kogin Bahar Aswad da ke kusa da tsibirin Cremia.

Jirgin yakin na Rashan na daga cikin manyan jiragen yakin kasar da ke shawagi a yankin tekun Bahar Aswad, kamar yadda gwamnan da Rasha ta nada a Cremia ya tabbatar, inda ya kara da cewa harin ya hallaka mutum 1 tare da jikkata mutum biyu.

Hukumomin Ukraine a wata sanarwar da suka fitar sun ce harin da suka kai da wasu makamai masu linzami, ba wai lalata jirgin ya yi ba, sun yi nasarar tarwatsa jirgin Rashan baki-daya. Kiev ta kuma tabbatar da cewa wasu kananan jiragen ruwan yakin Rasha guda 10 sun nutse a cikin tekun tare da asarar wasu jiragen yakin Rasha 16 tun bayan fara yaki tsakanin kasashen biyu.

Ukraine, ta ce za ta ci gaba da kai farmaki yankin har sai ta dawo da Cremia karkashin ikon ta daga mamayar Rasha.