Rasha: Fasinjojin jirgin da ya fadi sun rasu | Labarai | DW | 25.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha: Fasinjojin jirgin da ya fadi sun rasu

Rahotanni na cewar akwai yiwuwar fasinjoji da ke cikin jirgin nan na Rasha da ya yi hadari a tekun Black Sea sun rasu domin kuwa ya zuwa yanzu ba wani alamu da aka gani na wanda ke da rai a inda jirgin ya fadi.

Ma'aikatar tsaron Rasha din ta bakin kakakinta Igor Konashenkov ya ce masu aikin ceto sun tsamo gawarwaki na mutum goma kuma nan gaba za a tura gwanayen ninkaya kimanin 100 domin cigaba da laluben sauran wadanda hadarin ya rutsa da su. Jirgin dai ya fadi ne lokaci kankani bayan da ya tashi daga wani filin jirgin sama da ke birnin Sochi dauke da mutane 92 wadanda suka hada da sojoji da 'yan badujala da kuma 'yan jarida da ke kan hanyarsu ta zuwa kasar Siriya don gudanar da bikin sabuwar shekara a wani sansanin sojin Rasha da ke Siriya din.