Rasha da Amirka za su zauna kan Venezuela | Labarai | DW | 03.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha da Amirka za su zauna kan Venezuela

Manyan jami'an Rasha da Amirka za su ganan nan gaba kadan a yankin Turai dangane da bambarwar da ke wakana a kasar Venezuela. Kasashen biyu dai na da ra'ayi kan kasar.

Wani babban jami'i a Rasha, ya ce ministan harkokin wajen kasar Sergey Lavrov, zai gana da takwaransa na Amirka Mr. Mike Pompeo, inda za su tattanuawa kan bambancin da ke tsakanin kasashen biyu dangane da rikicin siyarar kasar Venezuela.

Ma'aikatar harkokiin wajen Rashar ta tabbatar da cewa manyan jami'an biyu za su gana ne a kasar Finland a tsakanin ranakun Litinin da kuma Talata na makon gobe.

Amirka dai na ganin sake zaben Shugaba Nicolas Maduro na Venezuela bara a matsayin ba daidai ba, abin da ya sanya kasar goyon bayan jagoran adawar kasar, Juan Guaido. Ita kuwa Rasha, na goyon bayan Shugaba Nicolas Maduro a dambarwar siyasar Venezuelar.