Kwamitin Kare Hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya, ya amince da kafa wani kwamiti da zai yi nazarin zarge-zargen take hakkin dan Adam din da ake yi wa Rasha.
Kasar Ukraine din ce dai ta mika wannan bukata ga kwamitin, inda mambobi 32 suka amince da ita yayin da Rasha da Iritiriya suka kada kuri'ar kin amincewa. Kasar Chaina na daga cikin kasashe 13 da suka yi rowar kuri'unsu, yayin amincewa da kudirin. Rashan dai ta ci gaba da musanta duk zarge-zargen da ake mata na cin zarafi da kuma take hakkin dan Adam din, a yakin da take da makwabciyarta Ukraine.