Rantsar da sabuwar majalisar ministoci a gwamnatin Buhari | Labarai | DW | 11.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rantsar da sabuwar majalisar ministoci a gwamnatin Buhari

A ranar larabar nan ce shugaban tarayyar Najeriyar Muhammadu Buhari zai rantsar da sabuwar majalisar ministocin kasar bayan jiran tsawon watanni biyar.

Ana san ran cewar nan ba da jimawa bane shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya zai bada sanarwar kafa sabuwar majalisar zartawar kasar da ke jagaba ta fuskar tattalin arzikin kasa a nahiyar Afrika.

Bikin rantsarwar dai zai gudana ne a farfajiyar Aso Rock dake a Abuja fadar gwamnatin Najeriyan.

Ministocin dai sun hada da kwarraru daga fagage da dama na cigaban jama'a da mafiya yawan 'yan Najeriya suke ma kallon ko shakka babu kwaliya zata biya kudin sabulu.