1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Putin ya gayyaci Trump zuwa Rasha

Yusuf Bala Nayaya
July 27, 2018

A lokacin da yake jawabi ga taron manema labarai sa'ilin da ya halarci taron kasashe da arzikinsu ke bunkasa cikin hanzari na BRICS, Putin ya ce akwai tsarin wata ganawar da Trump a cikin ajandarsa.

https://p.dw.com/p/32Dd4
Südafrika Johannesburg BRICS-Treffen Putin
Hoto: Reuters/Sputnik/A. Nikolsk

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana a wannan rana ta Juma'a cewa ya gayyaci Shugaba Donald Trump na Amirka zuwa birnin Moscow, ya ce shi tare da Trump na son sake tattaunawa duk da irin maganganu da ke zuwa su dawo a birnin Washington  bayan ganawar da aka yi tsakanin shugabannin biyu a birnin Helsinki a makon da ya gabata.

A lokacin da yake jawabi ga taron manema labarai sa'ilin da ya halarci taron kasashe da arzikinsu ke bunkasa cikin hanzari na BRICS, Putin ya ce akwai tsarin wata ganawar da Trump a cikin ajandarsa.

Ya ce tuni dama ya shirya sai dai batu na lokaci da inda za a sake haduwar a tattauna, amma shi tuni ya bude kofarsa ga Trump zuwa birnin Moscow. Putin dai ya ce tattaunawa tsakanin Amirkar da Rasha na da muhimmanci.