Pompeo da Maas sun gana a Moedlareuth | Labarai | DW | 07.11.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Pompeo da Maas sun gana a Moedlareuth

Gabanin cika shekaru 30 da rusa kantangar da ta raba yankunan biyu na Jamus, sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo ya gana da ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas, a marabar tsohuwar Jamus ta Yamma da ta Gabas.

Deutschlandbesuch von US-Außenminister Pompeo (picture-alliance/dpa/AFP/J. Macdougall)

Pompeo da Heiko Maas a Moedlareuth

Manyan jami'an gwamnatocin biyu na ziyartar kauyen Moedlareuth wadda aka raba biyu lokacin da Jamus ke rabe, inda yankin arewacinsa ya fada jihar Thuringia da ke tsohuwar Jamus ta Gabas, yankin kudancin kauyen kuma ke Bavaria da ke tsohuwar Jamus ta Yamma.

Wannan kan iyakar da aka fi tsananta tsaro lokacin yakin cacar baka, an rusa shi a yayin juyin juya hali cikin lumana a ranar 9 ga watan Nuwamban 1989.

Sakatare Pomoeo ya san wannan kauyen wanda ke da yawan mutane 50 kacal, a wanccan lokacin da ya zauna a Jamus a matsayin kwamandan rundunar soji a jihar Bavaria, lokacin yana matashi a shekarun 1980.