PDP: Rikicin cikin gida ya tsananta | Siyasa | DW | 23.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

PDP: Rikicin cikin gida ya tsananta

Rikicin cikin gida a babbar jamiyyar adawar Najeriya ta PDP na kara rincabewa inda tsofaffin ministocin jamiyyar suka nemi sabon shugaban jamiyyar Ali Modu Sherrif da ya sauka.

Rikicin jamiyyar PDP dai sun kara tsananta bayan nadin da aka yiwa tsohon gwamnan jihar ta Borno a matsayin shugaban jamiyyar ta PDP, domin kuwa rarabuwar kawunan da jamiyar ta so dinkewa daga samun sabon shugaban na kara yi mata nisa. Masu adawa da samuwar Modu Sherrif din dai na karuwa kama daga kwamitin amintattu zuwa ga wadanda suka kiran kansu da masu ceton jamiyyar.

Nigerianischer Präsident Goodluck Jonathan 11.11.2014

Dan takarar PDP a zaben 2015 ya sha kaye hannun jam'iyyar APC

To baya ga wannan, a yanzu kungiyar tsofafin ministocin jamiyyar tun daga 1999 zuwa yanzu sun ja daga da ma adawa da shugabancin na Modu Sherrif kamar yadda Tanimu Turaki tsohon ministan aiyyuka na musamman ya bayyana. A yanzu dai gwamnonin jamiyyar ne ke ci gaba da marawa shugaban jamiyyar ta PDP baya wadanda tun farko dama suka mara masa baya ya dare kujerar shugabancin jam'iyyar.

To sai dai ga kungiyar ceto jamiyyar PDP da suma suka ja daga na masu bayyana dalilansu na bukatar sabon shugaba ya yi murabus domin abin da suka kira ceto jamiyyar da ma dimukurdiyyar Najeriyar. A bayyane ta ke a fili rikicin da ya taso jamiyyar PDP a gaba na kara daukan sabon salo. Yanzu haka dai al'ummar Najeriya sun zuba ido don ganin za ta kaya game da wannan dambarwa.

Sauti da bidiyo akan labarin