Obama ya yabawa Faransa kan yakin Mali | Labarai | DW | 26.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Obama ya yabawa Faransa kan yakin Mali

Shugaba Barack Obama ya bayyana gamsuwarsa dagane da jagorancin Faransa a kokarin da sojin kasashen yammacin Afrika da na Faransan ke yi na karbe arewacin Mali.

French soldiers stand on a tank in Niono January 20, 2013. France and West African leaders called on Saturday on other world powers to commit money and logistical support for African armies readying their troops to join French soldiers already battling al Qaeda-linked militants in Mali. REUTERS/Joe Penney (MALI - Tags: CIVIL UNREST POLITICS MILITARY CONFLICT)

Französische Soldaten in Niono Westafrika

Obama ya furta hakan ne a wata zantawa da ya yi da shugaba Francois Hollande ta wayar tarho a jiya Juma'a, inda shugaba Obaman ya jaddada kudurinsa na tallafawa wajen ganin an magance aiyyukan ta'addacin a Mali din da kuma arewacin Afrika baki daya.

Baya ga batun ta'addanci a Mali da wasu kasashen arewacin Afrika, shagabannin biyu har wa yau sun tattauna dangane da halin da al'ummar Siriya ke ciki sakamakon yakin da ake tsakanin gwamnati da 'yan adawa inda shugabannin biyu su ka ce za su agazawa 'yan Siriya wajen ganin an samu sauyi a kasar.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Saleh Umar Saleh