Barack Obama shi ne bakar fata na farko da ya zama shugaban kasar Amirka, inda ya yi rantsuwar kama aiki a watan Janairun 2009.
Shi ne shugaban Amirka na 44. Bayan wa'adin farko, Obama ya sake samun wa'adi na biyu a zaben 2012. Ya samu kyautar zaman lafiya ta Nobel a shekarar da ya fara shugabanci.