Zaben rabin wa'adi na Amirka da sakamakonsa | Siyasa | DW | 08.11.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zaben rabin wa'adi na Amirka da sakamakonsa

An samu gagarumin fitowa a zaben rabin wa'adi na Amirka inda jam'iyyar Democrats ta lashe zaben majalisar wakilan Amirka inda Republican mai mulki ke da rinjaye a majalisar dattawa.

Zaben tsakiyar wa'adi a Amirka ya nunar da cewa jam'iyyar Democrats ke da rinjaye a zaben 'yan majalisar wakilai bayan samun kujeru sama da 220 daga cikin kujeru 435. Ita kuwa jam'iyyar Republican mai mulkin Amirka ke da rinjaye a majalisar dattawan kasar da kujeru sama da 50 daga cikin dari, kafin sakamako na karshe, matakin da ka iya jawo sauyin lamura a siyasar Shugaba Donald Trump.

DW.COM

Sauti da bidiyo akan labarin