1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cikas ga tawagar Trump a zaben Amirka

Lateefa Mustapha Ja'afar
November 6, 2018

Al'ummar Amirka sun shirya tsab domin kada kuri'a a zaben tsakiyar wa'adi na 'yan majalisun dokoki da ke gudana.

https://p.dw.com/p/37iJ7
USA Trump Yellowstone International Airport
Tawagar Trump ta yakin neman zabe ta gamu da cikas Hoto: Reuters/C. Barria

A yayin wannan zaben dai, za a sake zaben baki daya 'Yan Majalisar Wakilai su 435 yayin da za a sake zabar 'Yan Majalsar Dattijai guda 35 cikin mambobi 100 da majalisar ke da su. Wani kiyasi ya nunar da cewa jam'iyyar Republicans ta Shugaba Donald Trump ka iya rasa rinjayen da take da shi a yanzu haka a majalisar, inda ake hasashen cewa jam'iyyar adawa ta Democrats ka iya samun rinjaye a majalisun biyu. A hannu guda kuma da dama daga cikin gidajen talabijin din kasar ta Amirka da kuma kafafar sada zumunta ta Facebook sun ki yada yakin neman zaben tawagar da Shugaba Trump ke jagoranta cikin shirye-shiryensu, bisa kallon da suke masa na mai nuna kyama ga 'yan gudun hijira. Suma dai tashoshin NBC da kuma Fox News sun nuna cewa ba sa bukatar ci gaba da yada yakin neman zaben na Trump. Ita kuwa tashar CNN ta soki lamirin yakin neman zaben ne, inda ta bayyana shi da na nuna wariya da kyama.