1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon zaben na rabin wa'adi na Amirka

Yusuf Bala Nayaya Arthur Landwehr ARD
November 7, 2018

Zaben tsakiyar wa'adi a Amirka ya nuna jam'iyyar Democrats ke da rinjaye a majalisar wakilai bayan samun kujeru sama da 220 daga cikin kujeru 435 ita kuwa jam'iyyar Republican mai mulki ke da rinjaye a majalisar dattawa.

https://p.dw.com/p/37osd
USA Virginia Jennifer Wexton
Hoto: picture-alliance/AP Photo/The Washington Post/J. Chikwendiu

Zaben tsakiyar wa'adi a Amirka ya nunar da cewa jam'iyyar Democrats ke da rinjaye a zaben 'yan majalisar wakilai bayan samun kujeru sama da 220 daga cikin kujeru 435. Ita kuwa jam'iyyar Republican mai mulkin Amirka ke da rinjaye a majalisar dattawan kasar da kujeru sama da 50 daga cikin dari, kafin sakamako na karshe,  matakin da ka iya jawo sauyin lamura a siyasar Shugaba Donald Trump.

Nancy Pelosi
Hoto: Reuters/J. Ernst

Nancy Pelosi, da a baya shugabar marasa rinjaye a majalisar wakilan ta Amirka  ta tsinci kai a yanayi na farin ciki kasancewar a majalisar jam'iyyarta ta Democrats ta samu rinjaye abin da zai sa ta yi gaban kanta wajen neman sauyin lamura cikin kwanciyar hankali hakan kuma a cewar Pelosi zai sa dimukuradiyya ta kara samun karfi lamuran siyasa su daidaita a birnin Washington duba da wayar gari da aka yi da sabuwar Amirka wacce a majalisarta har da mata biyu Musulmai da ke shiga majalisa a karon farko wato Ilhan Omar 'yar shekaru 37 mai asali da Somaliya da Rashida Tlaib 'yar shekaru 42 mai asali da Falasdinu. A cewar Pelosi dai yanzu lokaci ya yi da hadin kai na jam'iyyarsu zai yi aiki wajen samar da waraka ga tarin matsaloli da suka dabaibaye siyasar ta Amirka.

Ga 'yan jam'iyyar Democrats wannan nasara babban lamari ne ganin cewa dama ce garesu su hana Shugaba Donald Trump yin gaban kansa yadda ya ga dama a shekaru biyu da ke tafe, za su iya hana wasu kudirori da zai gabatar gabansu wucewa, alal misali za su iya hanawa Shugaba Trump samun wasu kudade da yake bukata wajen muhimman aiyuka kamar kudin da ake bukata wajen gina katanga tsakanin Amirka da Mexiko, kuma ya zame wa Trump dole ya rika ba da bayanan komai a gwamnatinsa babu sauran boye-boye.

USA Halbzeitwahlen 2018 | midterms | Ted Cruz Texas
Hoto: Reuters/J. Bachman

Suma bangaren na Shugaba Donald Trump sun shiga murna da sakamakon da suka samu a zaben 'yan majlisar dattawan na Amirka wanda baya ga rike rinjaye a majalisar har da samun kari baxan fafatawa a wasu zabuka da suka hadar da wanda aka fafata tsakanin Beto O'Rourke na Democrats da Ted Cruz dan majalisa a jihar Texas.

Cruz dai ya fada wa gangamin magoya bayansa cewa nasara ce ga al'ummar ta Texas baki daya.

"Wannan nasara da muka samu, nasara ce ga maza da mata wadanda suka jajirce suka yi amfani da zuciyarsu da abin da suke so da lafiyarsu wajen ba da kariya ga Texas."

Donald Trump dai ya yi amanna cewa sakamakon zaben na rabin wa'adi shi ke zama izina ta makomar mulkinsa don haka ya sa himma wajen ganin ya yi yakin neman zabe ga 'yan majalisar jam'iyyarsa don samun nasara, sai dai kamar yadda kuri'ar jin ra'ayin jam'a ta nunar gabannin zaben amfani da batun 'yan gudun hijira don sanya tsoro a zukatan Amirkawa ya zama abu na uku inda mutanen na Amirka suka fi mayar da hankali ga batun inshorar lafiya da tsare-tsare na Trump baki daya.

USA Halbzeitwahlen 2018 | midterms | Demokraten in Washington
Hoto: Reuters/A. Drago

Wadanda suka fita kada kuri'ar dai sun fita da yawa fiye da shekaru hudu da suka gabata dukkanin 'yan takarar sun ja hankali na magoya baya don haka a cewat Sanata  Rick Santorum Trump ya cancanci yabo.

Sai dai duk da irin sauyin da aka gani na wannan zabe halayyar nan da aka gani shekaru biyu da suka gabata inda al'ummar birni da ke zaune cikin wadata su suka fi karkata kan 'yan Democrats yayin da kuma Trump da 'yan jam'iyyarsa suka samu tagomashi a kauyika.