1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta gargadi EU kan yarjejeniyar nukiliya

Abdul-raheem Hassan
January 15, 2020

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya ja kunnen kungiyar Tarayyar Turai kan ta guji daukar mumunan mataki kan yarjejeniyar nukiliyar 2015.

https://p.dw.com/p/3WEjI
Iran Teheran | Präsident Hassan Rouhani
Hoto: picture-alliance/AA/Presidency of Iran

Rouhani ya fadi haka ne bayan da kasashen Jamus da Faransa da Birtaniya suka matsawa Iran lamba kan yunkurin yin watsi da yarjejeniyar a baya-bayannan.

A watan Mayu shekarar 2019 Iran ta sanar da yin fatali da wasu muhimman ka'idojin yarjejeniyar da ta cimma da wasu kasahe shida a 2015, inda ta ce tuni ta zarta adadin Uranium da yarjejenaiyar ta ba da damar samarawa. Sai dai matakin Amirka na kashe wa Iran babban kwamandan soji, ya sa ta ayyana daukar matakin yin watsi da yarjejeniyar nukiliyar.