NPD za ta ci gaba da kasancewa halartatar jam′iyya a Jamus | Labarai | DW | 17.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

NPD za ta ci gaba da kasancewa halartatar jam'iyya a Jamus

Kotun tsarin mulki ta Jamus ta yi watsi da karan da aka shigar a gabanta na soke jam'iyyar NPD ta masu tsatsaura ra'ayi.

Dakin kolli na majalisar dokokin Jamus Bundesrat shi ne ya shigar da karan, kuma wannan shi ne karo na biyu tun daga shekara ta 2003 da ake gabatar da bukatar ta soke jam iyyar ta NPD.Sakamakon yadda ake yi ma ta kallon jam'iyyar da ke da manufofin 'yan Nazi, bayan wani kisan wariyar launin fata da wasu magoya bayan jami'yyar NSU suka yi a kan wasu bakin wacce ke kusa da jam'iyyar ta NPD.