1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazana mai girma ga tattalin arzikin Najeriya

April 29, 2021

Kamfanin NNPC ya ce Najeriya ba za ta samu kudin man da take dogaro da shi har na tsawon watanni uku ba, sakamakon tallafin man fetur da ya lashe kudaden shigan kamfanin.

https://p.dw.com/p/3slZT
BG Regierungssitze | Abuja
Hoto: Reuters/A. Sotunde

Duk da cewar dai mahukuntan kasar na tsallen murnar tashi na farashin danyen man fetur a kasuwannin duniya, a gefe daya dai tallafin tattace man da kasar ta dauki lokaci ta na shigo da shi na barazana ga makoma ta kasar da ke dogaro da bakar hajjar man.

Wata wasikar da  kamfanin man NNPC ya aike zuwa ga babban akawun kudi na gwamnatin tarraya dai ta ce, a watan Mayun da muke shirin shiga har ya zuwa Yulin da ke tafe dai kada  gwamnatoci a matakan kasar guda Uku su sa ran samun kudi daga kamfanin da ke zaman saniyar tatsa ga kasar.

Nigeria Selbstmordanschlag 28.07.2014
Tashar NNPCHoto: Reuters

Wasikar dai ta ce a cikin watan Afrilun da muke ciki dai kamfanin ya biya abun da ya kai  Naira miliyan dubu 111 da sunan tallafin man fetur da 'yan kasar suka sha a wata daya tilo.Najeriya.

Karin bayaniNajeriya: Hanyoyin fita daga matsalar kudi

Abun kuma da ya cinye daukacin gudummowar kamfanin ga kudade na rabo a tsakani na matakan mulkin kasar guda uku.

A yayin da  farashin man fetur  ke sauka a tashar jirgi na ruwa a farashin da ya kai Naira 184 kan ko wace lita daga waje, kamfanin na bada shi ga masu dillanci kan Naira 126. Abun da ke nufin ragin da ya kai na kusan Naira 60 kan ko wace lita ga kasar da ke shan lita Miliyan hamsin da doriya a kusan kullum.

Wannan ne dai karo na farkon fari da  tasiri na tallafin ke kara fitowa fili cikin kasar da ke tsaka mai wuya a samar da kudade na biyan albashi da aiyyukan yau dana gobe.

Karin bayaniMatatun mai masu zaman kansu a Najeriya

Koma ta ina ake shirin abi da nufin kaiwa ya zuwa samun tsira ga a'in da ke rama a halin yanzu, kasa da jihohin kasar guda biyar ne dai ke iya rayuwa ba tare da dogaro ga kudin shigar man fetur da harajin na Abuja da ake rabawa a duk wata a Abuja.

Ölgewinnung in Afrika - Symbolbild
Bututun man feturHoto: picture-alliance/A. Holt

Tarayyar Najeriyar dai na fatan fara aiki na matatar man fetur din Dangote a shekarar da ke tafe, na iya rage radadin rikicin ga kasar da ke karba da hagu sannan kuma ta mika a cikin hannun dama a cikin harkar man fetur.

Karin bayaniNajeriya ta sake shiga matsin tattalin arziki

Matatar da ke zaman irinta mafi girma a duniya dai zata samar da litar mai dubu 650 a kusan kullum, ko bayan sai da man da Naira ta kasar.