1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Rudani a kan karin farashin man fetur a Najeriya

Uwais Abubakar Idris MA
March 12, 2021

A Najeriya an shiga rudani a kan sabon farashin man fetur da hukumar daidaita farashin mai ta fitar amma kamfanin mai na kasa NNPC ya musanta, abin da ya sa kasuwar bayan fage tashi.

https://p.dw.com/p/3qYRG
Nigeria Tankstelle in Lagos
Hoto: AFP/Getty Images/E. Arewa

Rudani a kan farashin man fetur din dai ya jefa ‘yan Najeriya a hali na rashin tabbas a kan man da aka kwashe makwanni ana fuskantar karancin sa, wanda dama aka danganta da alamu na sake fuskantar kari.

Hukumar da ke kula da daidaita farashin albarkatun man fetur ta Najeriyar PPPRA ce dai ta fitar da sabon farashin man da ta ce a watan Maris za a sayar da kowace lita a  kan Naira 212, amma kuma  ‘yan sa‘o’i kalilan da sanar da hakan sai kamfanin mai na kasa NNPC ya ce wani babu batun kari. Tuni kungiyar kwadagon Najeriyar ta  maida martani tana cewa abin ya ba ta mamaki.

Nigeria Tankstelle in Lagos
Hoto: AFP/Getty Images/P. U. Ekpei

Gwamnatin Najeriyar dai ta bayyana mayar da harkar man fetur a hannun ‘yan kasuwa tare da tsame hannunta, amma ta ci gaba da sanar da ragi ko kari na farashin makamashin. A yanzu  dai kamfanin mai na kasar NNPC ne kadai ke shigo da mai kasar yayin da ‘yan kasuwa ke korafi.

 

Wakilin DW, Uwais Abubakar Idris, ya zagaya birnin Abuja inda ya iske galibin gidajen mai walau ba su da man ko kuma sun ki sayar wa jama’a, inda ‘yan bumburutu kuwa ke sayar da man da dan karen tsada.

Da alamun rudanin da wannan lamari ya haifar zai ci gaba da tasiri a kan hada-hadar man fetur a Najeriya, abin kuma da zai ci gaba da shafar rayuwar al‘umma musamman ma marasa karfi a da ta fi kowacce karfin arzikin man a nahiyar Afirka, kuma ta shida a duniya.