Nijeriya: Yinkurin tarwatsa gada a Lagos | Labarai | DW | 29.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nijeriya: Yinkurin tarwatsa gada a Lagos

A Najeriya hukumar 'yan sandar jihar Lagos ta sanar da yin nasarar karya wani yinkuri da kungiyar 'yan awaren Biafra ta yi na kai hari da bam kan gadar Mainland ko Mainland Bridge ta birnin Lagos. 

A cikin wata sanarwa da ya fitar kakakin hukumar 'yan sandar birnin na Lagos Don Awunah ya ce tun a ranar biyu ga watan Nuwamba suka kame wani mutum dan kabilar Ibo mai suna Abiodun Amos mai lakabin Senti haifaffen yankin Ese Odo na jihar Ondo wanda ke zama jagoran kitsa harin tarwatsa gadar inda suka yi nasarar karbo bindigogi biyu sanfarin AK-47 a maboyarsa da ke a unguwar Ikorodu ta birnin na Lagos. 

Hukumar 'yan sandar ta bayyana mutuman da cewar kwararre ne a fannin sarrafa kayayyaki masu fashewa da kera bama-baman gargajiya masu karfin gaske. Kuma bayanan da suka tatsa daga wurinsa ne bayan kama shi suka bai wa 'yan sandar damar kama wasu manyan kwalaye biyu na kayayyakin masu fashewa da kunamu 125 tayar da bam a cikin wata mota wacce ke shirin kama hanya zuwa saman gadar da za su tarwatsa.