1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Me ya kai Najeriya sayen fetur a Nijar?

Ubale Musa AMA(AS)
August 22, 2022

Gwamnatin Shugaba Buhari, ta kulla yarjejeniyar sayen tataccen man fetur daga Jamhuriyar Nijar, a wani yunkuri na cike gibin karancin mai da kasar ke fuskanta.

https://p.dw.com/p/4FsvF
Nigeria Tankstelle in Abuja
Hoto: AFOLABI SOTUNDE/REUTERS

Duk da takama da matatun man fetur guda hudu da kasar ke da su, Najeriya ta gaza fita daga kangin karancin mai, inda ake ganin dogayen layuka da ke zama ruwan dare game duniya, sai dai wata sabuwar yarjejeniya a tsakanin tarrayar Najeriya da makwabciyarta Nijar na shirin yin tasiri ga rage radadin karancinsa da ake fuskanta a Najeriya.

Idan har yarjejeniyar ta tabbata ta sayen tattacen mai daga matatar mai ta Soraz da ke Zinder a Nijar, ana hasashen samun sa'ida na matsalar fetur don taimakawa Najeriya, dalilan tsadar kudin dako a duniya da karuwar tashin farashin danyen mai su suka sa Najeriya karkatawa zuwa ga makwabciyarta Jamhuriyar Nijar.

Karin Bayani: Man Najeriya na tagomashi a kasashen Turai

A fadar shugaban hukumar gudanarwa ta NNPC Malam Mele kyari,"Najeriya na kan nemo hanyoyin wadatar mai a cikin kasar, ko baya gyara matatun mai da yunkurin gina wasu sabbi nan da gaba". Ganga dubu 15 daga cikin dubu 20 da matatar Soraz ke tacewa a rana na tafiya ne ga masu bukatar mai a wajen kasar, ciki har da 'yan kasuwar Najeriya kafin amincewa da taka rawar mahukunta na kasar.

Najeriya I Bututun mai l yankin Niger Delta
Bututun mai a Niger DeltaHoto: Friedrich Stark/imago

Hakan zai rage radadin bukatar man Najeriya da aka kiyasta lita miliyan 40 da doriya a kowace rana, kana masananna hasashen samun tataccen mai daga Nijar zai iya wadata yankin arewacin Najeriya da kuma habaka lamuran ciniki a tsakanin kasashen guda biyu.

Karin Bayani: Shirin farfado da tattalin arzikin Najeriya

Masana a fannin tattalin arziki kamar su Yusha'u Aliyu na ganin matakin zai kara inganta hulda a tsakanin kasashen biyu domin zai sa "Najeriya ta rage kudaden da take warewa na tallafin man fetur, kuma hakan zai sa Najeriya ta yi tunanin samun tsarin kafa wasu mamatun mai a yankin arewacin Najeriya, inda za ta iya sayen danyen mai maimakon tatacce daga Nijar".

Kasashen biyu sun kammada ra tsarin shimfida layin dogo da zai hada yankunan arewacin Najeriya da Nijar a wani mataki na karfafa hulda da habaka tattalin arzikinsu, baya ga wannan shirin na samar da tataccen man fetur daga jamhuriyar Nijar din mai makon saye daga wata kasa.