Nijar: ′Yan bindiga sun halaka ′yan yawon bude ido | BATUTUWA | DW | 09.08.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Nijar: 'Yan bindiga sun halaka 'yan yawon bude ido

Wasu 'yan bindiga dadi a Nijar sun halaka masu yawon shakatawa 'yan asalin kasar Faransa shida, tare da direbansu da kuma wani da ke yi musu jagora.

Rahotanni na cewa 'yan bindigan a kan babura sun kashe bakin ne a gabas da garin Koure da ke kusa a Yamai babban birnin kasar.

Hukumomi sun ce wannan ne karon farko da aka kai wa wani jami'in kasar Faransa hari a yankin, wanda ya saba karbar wadannan baki da galibi ke da sha'awar wajen saboda yawan rakuman dawa da ma wasu abubuwa na debe kewa.

Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa motar da 'yan yawon shakatawar ke a ciki lokacin harin mallakar wata kungiyar agaji ce ta kasar Faransa da ake kira ACTED.