1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A Nijar gwamnati na tattaunawa da 'yan adawa

Salissou Boukari MNA
October 31, 2019

A Jamhuriyar Nijar tun bayan da aka sanar da matakin komawa kan teburin tattaunawa tsakanin 'yan adawar da masu mulki, al'umma ke ba da shawarwari ta yadda kwalliya za ta biya kudin sabulu a fagen siyasar kasar.

https://p.dw.com/p/3SHyo
Firaministan Nijar Brigi Rafini da ke jagorantar tattaunawa tsakanin gwamnati da 'yan adawa
Firaministan Nijar Brigi Rafini da ke jagorantar tattaunawa tsakanin gwamnati da 'yan adawaHoto: Getty Images

Ana iya cewa dai wani sabon babi ne aka buda a kasashen Afirka renon Faransa na ganin kowane magabaci ya sasanta rikicin siyasar da ke kasarsa, domin an gani a kasar Senegal, Kamaru, Togo da Benin inda shugabannin wadannan kasashe suka yi hobbasa na zuba ruwa a wutar rikicin siyasar da ke kasashensu. To ko yaya ake ganin tasirin wannan haduwa da za ta yi? Sani Roufai mai sharhi ne kan al'amuran yau da kullum a Jamhuriyar Nijar.

"Tattaunawar za ta yi tasiri a Nijar tun da ta yi tasiri a wasu kasashen na renon Faransa. Musamman idan an yi wannan taron kasashen yamma za su bada taimako. Abinn da mutane suka saka ido su gani shi ne ko Shugaba Mahamadou Issoufou zai yi wa Hama Amadou afuwa. Da kuma sauran bukatu na 'yan adawa kan abin da ya shafi hukumar zabe." 

Niger Mahamadou Issoufou und Hama Amadou
Hama Amadou (a hagu) da Shugaba Mahamadou Issoufou (a dama) a shekarar 2011Hoto: BOUREIMA HAMA/AFP/Getty Images

Zaman na farko dai an yi shi ne ba tare da 'yan jarida ba, inda bangarorin da a da basa ga maciji da juna a fannin siyasa suka zauna domin fuskantar juna, wanda lamari ne da 'yan kasar ta Nijar suka jima suna jiran ganin ya auku.

Sai dai tuni aka bayyana yadda za a kafa kwamitin da zai jagoranci tattaunawar wadda bangaren masu mulki, 'yan adawa da ma 'yan baruwanmu kowa zai bada mutum goma-goma. Kungiyoyin kwadago mutum biyar, kungiyoyin fararan hula mutum uku. Akwai kuma Sarakuna mutum guda, Maluman Musulunci da na Kiristanci mutum guda-guda, sai kuma wakillan hukumar raya kasashe ta duniya da Tarayyar Turai.

Tuni a kan wannan batu na Nijar masana suka yi wannan duba na ganin an kafa wani kwamiti da ba na CNDP ba domin warware wannan rikici. Abdourahamane Ousmane shi ne tsohon shugaban hukumar sadarwa ta kasar Nijar CSC da yanzu ke bada gudunmawa kan harkokin zabe a kasashe da dama na Afirka.

Ibrahim Yacouba tsohon ministan harkokin wajen Nijar kuma daya daga cikin 'yan adawa
Ibrahim Yacouba tsohon ministan harkokin wajen Nijar kuma daya daga cikin 'yan adawaHoto: DW/N. Amadou

"Abubuwan da za su amfani kasar Nijar ya kamata a sa gaba. Kasa ta yi zabe cikakke, zaben da ba zai kawo gardama ba. na yi imani idan aka samu yarjejeniya za a yi zabe ba tare da tashin hankali ba."


Su ma matasa ba a barsu a baya ba, domin kuwa "yin sulhu tsakanin 'yan siyasar Nijar batu ne da kowa ke begen gani", a cewar Assamaou Mahamadou mamba a jam'iyyar matasa ta SDR da ta kara da cewa ya kamata a sanya mata masu yawa a cikin wannan kwamiti.

A halin yanzu dai kallo ya koma ga kwamitin da za a kafa da kuma gwamnati da za ta bada damar komai ya gudana har a kai ga cimma burin da aka sa wa gaba na sasantawa.