Nijar ta yi tir da sayar da bakin hauren Libiya | Siyasa | DW | 17.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Nijar ta yi tir da sayar da bakin hauren Libiya

Jamhuriyar Nijar ta nuna takaicinta kan cinikin bakin hauren Afirka da wasu bata gari ke yi a kasar Libiya, inda ta ce ya saba wa dokokin kasa da kasa.

Gwamnati Jamhuriyar Nijar ta bayyana matukar damuwarta kan dabi'un da ake nuna wa bakin haure a kasar Libiya inda a baya- bayannan rahotanni suka ce 'yan baranda a Libiya na sayar da su a matsayin bayi, lamarin da ya harzuka gwamnatin Nijar saaboda galibin bakin hauren na bi ta kasar don zuwa Turai ta barauniyar hanya .

Cikin wata sanarwa da fitar ma'aikatar harkokin wajen Nijar ta yi kira ga gwamnatin Libiya da kuma Majalisar Dinkin Duniya da su dauki matakan kawo karshen cinikin bakin haure cikin hanzari kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanada. Sannan hukumomin na Niamey sun bukaci ofishin jakadancinsu a Libiya da ya gudanar da bincike don ganin girman matsalar.

Jamhuriyar Nijar na daya daga cikin kasashe da aka kasa kawar da bauta kwata-kwata a Afirka. Sannan 'ya'yata da dama na zuwa cin rani a kasar Libiya

Sauti da bidiyo akan labarin