Nijar ta mayar wa Amirka martani | Labarai | DW | 13.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nijar ta mayar wa Amirka martani

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta mayar da martani kan zargin da wasu daga cikin shugabannin sojin Amirka a Nijar suka yi na cewa ba a rasa hadin bakin al'ummar kauyen Tongo-Tango na kan iyaka da Mali ba.

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta mayar da martani kan zargin da wasu daga cikin shugabannin sojin Amirka a Nijar suka yi na cewa ba a rasa hadin bakin al'ummar kauyen Tongo-Tango na kan iyaka da Mali ba, a harin da wasu 'yan ta'adda suka kai wa ayarin sojojin Nijar da na Amirka a yankin a makon da ya gabata inda suka kashe sojoji takwas da suka hada da na Amirka guda hudu.

A wata hira da ya yi da tashar DW a wannan Juma'a, ministan cikin gida na jamhuriyar Nijar Malam Bazoum Mouhamed ya bayyana cewa suna da tabbacin cewa al'ummar yankin na kyamar wadannan 'yan ta'adda duk da ya ke ba za a rasa baragurbi a cikinsu ba.

Wasu kafofin yada labarai na kasar ta Amirka ne dai suka ruwaito labarin da ke cewa shugabannin rundunar sojin Amirka a Nijar ta zargi al'ummar kauyen na Tongo-Tongo da bai wa 'yan ta'addan bayanai ga kasancewar sojojin a yankin nasu.