1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sauyi a bangaren hakar man fetur a Nijar

Gazali Abdou Tasawa MAB
April 23, 2024

Hukumomin mulkin soja na Jamhuriyar Nijar, sun gudanar da sauye-sauye ga tsarin aikin man fetur da nufin kare hakokin kasar da ma hana ci da guminta da wasu kamfanonin man fetur na ketare ke yi.

https://p.dw.com/p/4f6gj
Nijar | Gwamnati | Sojoji | Janaral Abdourahmane Tchiani
Shugaban gwamnatin mulkin sojan Jamhuriyar Nijar Janaral Abdourahmane TchianiHoto: CNSP

Sababbin matakan da hukumomin Jamhuriyar ta Nijar suka bijiro da su sun hadar da haramta wa kamfanoni bayar da kwangilar duk wani aiki da kamfanoniko ma'aikata 'yan kasa za su iya yi, ga kamfanoni ko kuma ma'aikata daga kasashen ketare. Matakin hukumomin Nijar din dai na zaman wani tsari da suke son su bi sannu a hankali da suke dauka, wajen mayar da kamfanonin hakar man fetur din ga kasar.

Karin Bayani: Nijar ta ciyo bashin kudi daga Chaina

Yayin wata ganawa da ministan man fetur na Jamhuriyar ta Nijar Mahaman Moustapha Barke Bako ya yi da shugabannin kamfanonin CNPC da Savannah da Sipex da ke aikin hakar man fetur a kasar, ya sanar da su wadannan sababbin matakai da hukumomin mulkin sojan karkashin jagorancin Janaral Abdourahmane Tchiani suka dauka na tsarkake tsarin aikin hakar man fetur a kasar ta yadda za ta fi cin moriyar arzikinta ba tare da ta bari kamfanonin na ci da guminta ba.

Nijar | Areva | Faransa | Arlit | Uranium
Baya ga man fetur, Nijar na da arzikin makamashin uraniumHoto: Maurice Ascani/Areva/AP Photo/picture alliance

Sababbin matakan sun kuma tanadi tilasta kamfanonin man fetur din na ketare daukar ma'aikata kai tsaye, ba tare da bi ta hanyar wani kamfanin daukar ma'aikata ba. Haka kuma hukumomin mulkin sojan Nijar sun sanar da shirin daukar cibiyar bincike mai zaman kanta ta kasa da kasa wacce za ta yi bitar aikin binciken da aka yi a kan yadda aka tafiyar da hakar man fetur a tsawon shekaru a kasar, domin tabbatar da sahihancin binciken da aka yi a baya. Tuni dai kungiyar ROTAB ma sa ido kan aikin hakar ma'adanai a Nijar din, ta bakin Boubacar Ilyassou Shata ta bayyana gamsuwarta da matakin gwamnatin.

Karin Bayani: Matsalar ruwa a garin Zaouzawa na Nijar

To sai dai a nasa bangare Malam Sahanin Mahamadou mai adawa da mulkin soja a Nijar din, na ganin sauye-sauyen da hukumomin sojan suka yi tamkar wani sabon wayon a ci ne na karkatar da akalar arzikin man fetur din. Hukumomin mulkin sojan na Nijar sun kuma sanar da bitar kwangilar raba arzikin mai tsakanin Nijar da kamfanonin, domin tabbatar da ba a ci da gumin kasar ba. Kazalika sun sanar da kamfanin WAPCO mai kula da bututun jigilar danyan man Nijar zuwa tashar Ruwan Cotonou shirin aika tawagar kwararru, domin bincika da kuma tabbatar da yawan man da ke fita. Kamfanin a nasa bangaren, ya sanar da  binciken jiragen ruwan dakon man fetur din Jamhuriyar ta Nijar.