1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin tace man fetur din Jamhuriyar Nijar a Najeriya

Abdoulaye Mamane Amadou MA
February 14, 2017

Jamhuriyar Nijar ta bayyana aniyar kulla yarjejeniyar tace danyen manta a Najeriyar a kokarin rage kaifin karancin man fetur a jihohin arewacin Najeriya.

https://p.dw.com/p/2XXqu
Nigeria Port Harcourt Arbeiter auf Plattform Ölförderung
Hoto: Getty Images/AFP/P. Utomi Ekpei

Tun a tsakiyar shekarar bara ne dai tarayyar Najeriya da Jamhuriyar Nijer suka fara tunanin bullo da sabuwar dabarar shimfida layin bututu danyen mai da zai tashi daga kudu maso gabashin kasar don kara karfafa bukatar samun wadataccen man fetur da dangoginsa a arewacin Najeriya inda matatar man fetur ta Kaduna za ta gudanar da aikin tace shi da kuma samar da shi ga al'uma.
Ko da yake har yanzu bangarorin biyu ba su kai ga rattaba hannu a kan yarjejeniyar ba, bincike ya tabbatar cewa tuni aka yi nisa wajen samar da wannan fasahar da ke zama irin ta ta farko ga wasu kasashen Afirka don cin moriyar tattalin arzikin junansu.

Yayin da yake ganawa da manema labaru Ministan albarkatun man Nijer Malam Foumakoye Gago ya tabbatarwa DW da cewar yanzu hakan ana dab da kulla wannan yarjejeniya ne. A cewarsa ana nazari a kai, sai dai akwai wani mataki na gaggawa da ake son dauka kan aikin matatar. A cewarsa yana iya daukar shekaru biyu misali, amma abin da ake son yi shi ne ita matatar man ta Soraz za a yi mata wani gyaran fuska ta yanda maimakon ganga dubu 20 da ake fitowa da su ko wace rana za soma amfani da na'urori masu karfi don kara hako ganga dubu 40, inda za a'a dauki man ganga dubu 20 cikin manyan motocin dakon kaya a kai Kaduna a cikin dan lokaci. Da jumawa ne dai gwamnatin Jamhuriyar Nijer ta nuna bukatar fitar da danyen man fetur din da take samarwa daga yankin Agadem zuwa mahakar man Kribi dake kasar Chadi, sai dai faduwar darajar man a kasuwannin duniya da tashin Dalar Amirka sun kawowa bukatar cikas abubuwan da suka tilastawa Nijer hangen wasu kasashe mafi kusa da ke iya amfani da dimbin man na ta.

Niger Ölminister Foumakoye Gado
Ministan man fetur na Nijar Foumakoye Gado ya ce a cikin watan nan na Fabrairu za a fara kai man Nijar zuwa Kaduna don tace shiHoto: DW/A. M. Amadou
Ölplattform in Nigeria
Guda daga cikin matatun man fetur a NajeriyaHoto: AP

Ministan na albarkatun man fetur na Nijer, ya ce an yi tsammanin ko a cikin wannan watan na Febrairu ma za a fara daukar danyen man cikin motoci don kaiwa Kaduna, to amma akwai wasu takardu masu yawa da kuma gyare gyaren bututun man Nijer da mahakar man kasar da kuma matatar mai ta kaduna don shi ne har yanzu abin ya gaza girkuwa, sai dai ya ce ba shi ne ya sa aka makara ba, saboda ana son a hanzarta fara daukar danyen man zuwa Kaduna kafin karshen wannan shekarar. Tuni ma dai masu sharhi kan harkokin tattalin arziki da al'amuran yau da kullum ke ci gaba da tsokaci kan yunkurin kulla yarjejeniyar, duk da yake kasashen biyu za su iya cin moriyar yarjejeniyar. Yayin da wasu masana harkokin mai ke ganin kamata ya yi kasashen biyu su kiyaye.