1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru biyu da fara hako man fetur a Nijar

November 28, 2013

Gwamnatin Nijar ta nunar da cewa kasar ta fara cin gajiyar arzikin man fetur da Allah ya hore mata. Sai dai wasu kungiyoyi masu zaman kansu da talakawa suka ce ba su fara gani a kasa ba..

https://p.dw.com/p/1AQH9
In Glasflaschen abgefülltes Benzin wird an einer Straße in der Stadt Maradi im Süden des Niger angeboten, aufgenommen am 04.11.2007. Das Benzin wird so portioniert zumeist an Moped- und Motorradfahrer verkauft. Das südlich der Wüste Sahara in der Sahelzone gelegene westafrikanische Niger gehört zu den ärmsten Ländern der Welt. Foto Thomas Schulze +++(c) dpa - Report+++
Hoto: picture-alliance/ZB

Ranar 28 ga watan Nowambar 2011 ne Nijar ta shiga sahun kasashen duniya da ke da arzikin man fetur, bayan kaddamar da matatar mai da aka fi sani da suna SORAZ a Damagaram. An shirya za ta dinga bayar da ganga dubu 20 na fetur a kowace rana ta Allah domin amfanin al'umar kasar tare da sayar da shi ga wasu kasashe makwabta.

Sai dai wannan batu na ci-gaba da haifar da muhawara a tsakanin gwamnatin da 'yan kasar dangane da tasirin da samun wannan arziki ya yi ga tattalin arzikin Nijar dama rayuwar al'umarta. Malam Nouhou Arzika shugaban kungiyar farar hula ta MPCR na ganin cewa ya zuwa yanzu kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.

TO GO WITH AFP STORY IN FRENCH BY Boreima HamaPeople look at produce at a market in Niamey on January 30, 2011, on the eve of Presidential elections seen to turn a page on a year of military rule following the military coup against Niger's then President Mamadou Tandja in February 2010. The Sahelian country's 6.7 million registered voters must choose between three former allies of deposed Tandja and a longtime opponent of the former leader Mahamadou Issoufou to head the country shadowed by the growing threat of Al-Qaeda militants. AFP PHOTO / BOUREIMA HAMA (Photo credit should read Boureima HAMA/AFP/Getty Images)
Wasu talakawan Nijar ba su yarda cewa sun fara cin gajiyar fetur baHoto: B.Hama/AFP/GettyImages

Ya ce "Burin da muka yi na kasa ta yi amfani da wannan man fetur da Nijar ta samu domin mu daina zuwa bara, haka ba ta cimma ruwa ba. Kudin da suka samu sai kawai anan hada hada: magabata ne su ke kirkiro da hanyoyin satar kudi.a Ayanzu haka akwai sabbin masu kudi da aka samu a cikin gwamnati da wasu sauran manyan hukumomi da aka sanya. "


Ra'ayoyi sun sha ban-ban kan man fetur a Nijar
Kusan al'umar Nijar baki daya ne suka kasance a cikin farin ciki a lokacin kaddamar da wanann aiki na soma hako man fetur kasar tasu. Sai dai wani mazunin birnin Yamai ya ce " har yanzu ba mu gani a kasa ba. Abun da muka saba sha a kullum,har yanzu haka shi muke ci-gaba da sha mu talakawa." Sai dai wani dan Nijar da DW ta tattauna da shi ya nuna gamsuwarsa a kan man fetur, inda ya ce "kullum man fetur ba ya yankewa a kasuwa, har ma a kauyuka ana samunshi."


Gwamnati ta ce an fara cin gajiyar fetur a Nijar

A lokacin da ya ke mayar da martani a kan wadannan korafe- korafe, ministan da ke kula da harkokin man fetur na Nijar Foumakoy Gado ya nunar da cewa a zahiri NIjar na amfani da arzikin karkashin kasa da Allah ya hore mata. Ya ce " A shekarar da ta gabata ganga dubu 12 kawai muke samu a kowace rana, amma a wannan shekara, kudaden da wanann aiki ya shigar aljihun gwamnati ya kai miliyan dubu 94 kuma a bana muna sa ran za a kai miliyan dubu 100 ko 110."

Niger eng
Ana ci-gaba da gano rijiyoyin fetur a wasu sassa na Nijar

Wasu sabbin bincike da aka gudanar a Nijar a baya-bayan nan a yankin Agadem ya nunar da cewa yawan fetur da aka gano ya tashi daga ganga miliyon 300 zuwa ganga miliyon 600 a shekara. Kuma ana sa ran cewa zai kai ganga miliyan dubu nan da wani lokaci. Hakazalika a cikin yankin Tenere da Bilma bincike ya gano cewa akwai wani karin man fetur da ke binne a cikinsu.

Mawallafi: Gazali Abdou Tasawa
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe