1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Matsalar ruwa a garin Zaouzawa

March 23, 2021

A yayin da ake ci gaba da bikin ranar ruwa ta duniya da Majalisar Dinkin Duniya ta ware, a Jamhuriyar Nijar mazauna garin Zaouzawa da ke makwabtaka da wajen zuba gubar man fetir din kasar sun koka kan matsalar ruwan sha.

https://p.dw.com/p/3r0oX
Trinkwassser an Schule in Burundi
Al'ummar Zaouzawa da ke Damagaram a Jamhuriyar Nijar na fama da rashin ruwan shaHoto: picture-alliance/dpa/T. Schulze

Taken ranar  ruwan ta bana dai wacce ta dauko tushe tun shekarar 1993 shekaru 28 da suka gabata kenan, shi ne abin da ruwa ke nufi ga mutane da irin kimarsa da kuma yadda za'a iya kare wannan mahimmiyar kyauta. To sai dai ganin samar da tsaftataccen ruwan sha ga al'umma nauyi ne da ya rataya a wuyan shugabanni, a wanan karni ruwa da ake ma taken abokin aiki inji yan karin magana, a garin Zaouzawa da ke makwabtaka da inda kamfanin tace man fetir din kasar na SORAZ ya tanadi runbun tsimi na gubar man fetir, al'umma na fama da matsalar ruwa.

Matsalar ruwan sha a Nijar

Yayin da wakilan tashar DW suka kai ziyara garin na Zaouzawa, sun riski cincirindon mata da kananan yara  dauke da jarkoki a bakin fanfon garin kwaya daya tilo da ake da shi a garin, inda wakilin rabon ruwan ya ce a irin wanan lokaci na shigar bazara fanfon na kafewa. Hakan ya sanya al'ummar garin ke hada kai wajen hana bai wa dabbobi ruwan fanfon sai dai na rijiya. A yanzu dai talakawan sun zura na mujiya  kuma sun kasa na zomo, suna jiran lokacin da za su yi bankwana da wanan matsala.