Nijar: Sallamar wasu hafsoshin sojoji kan zargin yukurin juyin mulki | Siyasa | DW | 22.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Nijar: Sallamar wasu hafsoshin sojoji kan zargin yukurin juyin mulki

A Nijar an kori wasu manyan hafsoshin kasar da aka zarga da shirya makarkashiyar yunkurin juyin mulk.

Ko da yake da farko hukumomin kolin kasar ta jamhuriyar Nijar ba su fito suka bayyana matakin korar manyan hafsoshin biyu ba, amma daga bisani kakakin gwamnati Asoumana Malam Issa ya tabbatar wa waklinmu na Yamai Abdoulaye Mamane Amadou ta wayar tarfo labarin koran hafsoshin sojan. Tun farko dai wasu kafafen yada labaru masu zaman kansu suka wallafa labarin. Kafafen yada labarun sun bayyana cewar matakin ya shafi wasu manyan hafsoshin biyu da suka hada da Chef de bataillon Oumarou Issifi tsohon babban kwamandan rundunar sojan kasa da ke rike da manya-manyan makamai a yankin Tillabery, da kuma wani hafsan Laftanan Ousmane Awal Hambali da tuni iyallansa da suka tabbatar da matakin ta hanyar wata takardar da suka ce an kai wa matashin hafsan sojan har a gidan yarin da yake tsare a garin Say.

Ko yaushe za su gurfana gaban kotu?

Daukacin hafsoshin dai ana zaginsu ne da aikata laifi musamman ma yunkurin kifar da gwamnati wanda shugaban kasa da kansa ya fito ya ambata a wani jawabinsa na 'yan kasa a ranar 17 ga watan Disamban 2015.

Niger Moussa Aksar Investigativ-Journalist

Moussa Aksar dan jarida kuma mai bincike

Tuni dai bangarori dabam-dabam suka fara tofa albarkacin bakinsu kan matakin. Malam Moussa Aksar dan jarida ne kuma mai sharhi a fannin tsaro.

Ya ce: "Zan iya cewar takardu sun riga sun fito an dauki matakai game da duk abinda ya faru har aka zo ga laifuffukan da suka aikata wanda kwamitin ya fadi kuma daga baya aka dauki matakan korarsu daga aikin soja, to ina batun shari'a? Zan iya cewa wannan matakin irin wanda ake dauka ne takwana kafin a kai ga shari'a."
A wani shafin takardar da iyalan gidan Ousmane Awal Hambali suka bai wa tashar DW ya yi nuni da cewar hukumomin kolin kasar sun dauki matakin ne tun a farkon watan Janairun wannan shekarar, abubuwan da suka sa jama'a da dama nuna matukar damuwarsu kan rashin fitowa fili a yi wa 'yan kasa bayani.

Rufa-rufa kan batun

Malam Lawali Aboubakar wani dan gwagwarmaya ne da ke rajin kare hakin dan Adam.

Ya ce: "Ba wai fitar da mutum aikin soja ba ko kuwa kama mutum a tsare shi ba a'a abinda ake bukata shi ne 'yan kasa su san wane irin zargi ne ake zarginsu da shi: A fiddo sanarwa 'yan kasa su sani wadda babu wani rudani a cikinta."

Niger Soldat an der Grenze zu Nigeria

Sojojin Nijar a fagen yaki da Boko Haram a Diffa

A tsakiyar watan Disambar shekarar bara ne dai hukumomin jamhuriyar Nijar suka ambata bankado wata makarkashiya ta yunkurin yi wa shugaban kasar juyin mulki a kan hanyarsa ta dawowa daga Maradi, yunkurin da ya yi sanadiyar kama dimbin manya hafsoshin sojan kasar da wasu farar hula galibinsu 'yan siyasa da ake zargi da yin gamin baki da sojan don kifar da gwamnati.

Sai dai jama'a sun yi ta musanta wannan zargi musamman ma 'yan adawa suna masu cewar bita da kulli ce kurun irin ta siyasa. A yayin wani taron manema labaru da Ministan tsaron Nijar ya jagoranta na lokacin Malam Karidjo Mahamadou ya tabbatar da zargin kana ya ambato kafa wata kotu ta musamman da ta fara zamanta a tsakiyar watan Maris don soma shari'ar. Sai dai har ya zuwa yanzu babu wasu cikakkun labarai a kan gundarin shari'ar.

Sauti da bidiyo akan labarin