Nijar: Sabon kawancen sauya fagen siyasa | Siyasa | DW | 11.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Nijar: Sabon kawancen sauya fagen siyasa

Wasu jam’iyyun siyasa da na kungiyoyin farar hula sun kulla wani sabon kawancen FDCP da zummar yin gwagwarmayar sauya fagen siyasar Nijar.

Niger Niamey Opposition

Jerin gwanon 'yan adawa a lokutan baya

Sabon kawancen dai mai suna Front Democratique Pour le Changement Politique FDCP a takaice ya tattara wasu 'yan farar hula ne da 'yan siyasa a kasar ta Nijar. Kana shugabanninsa sun ce wannan kawancen dai ya bayyana ne da zummar inganta fagen siyasar Nijar din mai kunshe da rudani kala-kala da kuma ake ganin sannu a hankali yake daukar wani sabon salon. Yanzu haka ma har ta kai ga 'yan siyasar kasar daukar wasu miyagun tabi'o'in da suka saka kasar yin kwan gaba kwan baya a fannoni daban na cigaba da kyautata rayuwar talakawanta bayan ba su wata cikakkiyar amana yau sama da shekaru 25.

Malam Soumaila Amadou shugaban jam'iyyar PND Awaywaya ne kuma daya daga cikin wadanda suka girka kawancen ya ce lokaci ne ya yi da talakawan Nijar suka fara nuna gajiya da tabi'un na 'yan siyasa.

"Halin da suka jefa kasar nan ai ga shi nan a fili tun kafin a fara demukradiyyar ai cewa aka yi akwai Uranium, aka dawo aka ce muna da zinariya, muka dawo aka ce muna da man fetur. To amma duba ka gani yau wane ne ya sake, mi ya sake? Kasa ba ta sake ba, su ne kawai suka sake kuma yau an komo ana wata siyasar da in aka sake aka zura masu ido, sun mayar da ita ramuwar gayya. To ni din ma na yarda idan har guguwar canjin nan in ta tashi ta wuce da ni, na yarda. Kalli akwai yanzu jam'iyyun siyasa sama da 70 a kasar nan, ni ko na san yau ko Chana aka kasata gida 70 karfinta ragewa zai yi. To a hakan za'a cigaba?"

Kwadayin 'yan siyasa ya fito fili

Proteste der Zivilgesellschaft im Niger

Zanga-zangar kungiyoyin farar hula don adawa da tsadar rayuwa

Kawancen ya ce wasu ababen da suka wakana a baya-bayan nan musamman ma a gabanin zabubbukan da aka yi, sun kara fitowa karara da kwadayin 'yan siyasar ta Nijar da ma nuna kasawa, kuma suka ki janyewa don bai wa wasu damar dorawa daga inda suka kasa.

"Sun ce ba su yarda da gwamnatin nan ba, sun ce ba su yarda da sakamakon zabe da duk hukumomin da za su fito daga ciki ba. Da aka yi wani abu kwarab sai ga su suka ce ai daga gobe 'yan majalisunsu su je kuma za su je zaben kananan hukumomi. Muka ce ahhh yaya ne za mu gamu da mace a kan kwana ta ce ba ta da miji, kuma bayan mun sha wata kwanar ta ce ita matar aure ce, wane irin zance ne wannan?"

To ko yaya 'yan farar hular da ke fafatukar kare demukradiyya suka ji da irin wannan kawancen? Malam Nasirou Seidou shugaban rukunin wasu kungiyoyi ne na muryar talaka.

Niger Amtseid des neu gewählten Präsidenten Mahamadou Issoufou

Shugaba Mahamadou Issoufou lokacin rantsuwar kama aiki a wa'adin mulki na biyu

"Gungu ne wanda idan har akwai hanyoyin da za'a bi a cikin demukradiyya da doka a sauya abin da suka ce cikin lumana da girmama dokokin kasa, yana da kyau. Sai dai ina tsoron da ajiye tambaya shi ne wai kaka ne za'a canza a kasar ga halayen 'yan siyasa da ma su mayan 'yan siyasar gaba daya su kansu?"

Ba a bukatar kawancen 'yan siyasa da farar hula

A yayin da Malam Nasirou Seidou ke ajiye dimbin ayoyi kan yadda kawancen da ya ce zai kawo sauyi a fagen siyasa, ga Malam Son Allah Dan Badji na kungiyoyin CADED, matsalar Nijar a yanzu halin da take ba wai ta kulla kawancen jam'iyyun siyasa ba ne da na 'yan farar hula.

"Ba abu ne da zai kai Nijar gaba ba don ma hakan na cikin abubuwan da ake ganin zai ci amanar talakawa tun da su talakawa ba wai wani gungu-gungu suke son a yi ba, a'a."

Jamhuriyar Nijar dai tasha samun kawace kala-kala da kowane ya fito yake nuna cewar zai yi kokuwa ne don inganta demukradiyya. Sai dai wasu lokutan tafiyar ta kawancen kan kasance mai rauni wanda wani bi takan kai ga kawancen kan sanya kira wadanda ake yin gwagwarmayar don su, su kasa fitowa don yin rakiya.

Sauti da bidiyo akan labarin