Nijar na yin tankade da rairaya bisa ta'ddanci
February 17, 2015Talla
Nijar dai ta shiga rundunar hadaka tare da Kamarun da Chadi, don kawar da mayakan kungiyar Boko Haram, inda ita kuwa kungiyar Boko Haram ta maida martani da kai wa dukkan kasashen hare-hare. A Najeriya ma dai sojojin kasar sun sanar kame garin Munguno a jiya Litinin, sai dai fa 'yan Boko Haram sun kaddamar da hari cikin kasar Kamarun, inda suka hallaka sojojin Kamaru biyar.