Nijar: Kashe-kashen Boko Haram a Diffa | Labarai | DW | 07.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nijar: Kashe-kashen Boko Haram a Diffa

Wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta wallafa a jiya Juma'a na cewa, akalla fararan hulla 177 ne aka kashe sakamakon hare-haren kungiyar Boko Haram a Jamhuriyar Nijar.

Rahoton kuma ya ce wasu fararan hullan 137 suka samu raunuka daga watan Fabrairu na 2015 zuwa Satumba na 2016 a yankin jihar Diffa da ke Kudu maso gabashin kasar ta Nijar mai makwabtaka da Tarayyar Najeriya. Rahoton ya ce wasu mutanen 13 fararan hullan sun yi batan dabo, yayin da wasu guda hudu aka tabbatar cewa 'yan kungiyar Boko Haram ne suka tafi da su. Ofishin hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da harkokin agaji na OCHA reshen kasar ta Nijar ne ya wallafa wannan rahoto ta shafinsa na Internet, inda ya ce wannan adadin bai shafi hare-haren 'yan kungiyar na tsakanin watan Octoba na 2016 kawo wannan wata na Janairu ba.

Sai dai rahoton bai bada adadin sojoji da suka mutu ko kuma na 'yan kungiyar Boko Haram da aka kashe ba. Amma ya yi karin haske cewa a Gundumar Bosso kadai mayakan na Boko Haram sun kashe fararan hulla 101, yayin da suka jikkata wasu 42, uku sun bace sannan biyu an tafi da su. Sannan a Gundumar Diffa an kiyasta fararan hulla 64 da aka kashe, wasu kuma 90 suka samu raunuka, sai kuma Gundumar N'Guigmi dukanninsu cikin jihar ta Diffa nan kuma an kashe fararan hulla 12 tare da likkata uku, sannan 10 ba a san inda suke ba. Jihar ta Diffa dai na dauke da 'yan gudun hijira da yawansu ya zarta mutum 300.000 a cewar Majalisar Dinkin Duniya.