1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Nijar: Ina makomar Jam'iyyar PNDS Tarayya?

Gazali Abdou Tasawa
May 1, 2024

Baraka ta kunno kai a Jam'yyar PNDS Tarayya tsakanin magoya bayan hambararren shugaba Bazoum Mohammed da na tsohon shugaba Mahamadou Issoufou, sai dai wasu magoya baya na kira a yi sulhu

https://p.dw.com/p/4fP3J
Niger Mahamadou Issoufou und Mohamed Bazoum
Hoto: Aboubacar Magagi

A Jamhuriyar Nijar a daidai lokacin da baraka ke kara girma tsakanin magoya bayan hambararren shugaban kasa Mohamed Bazoum da tsohon shugaban kasa Mahamadou Issoufou, da kuma ke barazana ga makomar jam'iyyar PNDS Tarayya, wacce sojoji suka kifar da mulkinta, wasu 'yan kasar masu kusanci da shugabannin biyu, sun soma kiraye-kiraye na ganin bangarorin biyu sun shafa wa zuciyoyinsu ruwa domin yin sulhu a tsakaninsu. 

Mahamadou Issoufou da Mohamed Bazoum
Mahamadou Issoufou da Mohamed BazoumHoto: Aboubacar Magagi

Tun dai bayan cece-kuce da ya barke a baya bayan nan tsakanin magoya bayan hambararren shugaban kasa Mohamed Bazoum da tsohon shugabn kasa Alhaji Mahamadou Issoufou, bayan da diyar hambararren shugaban kasar a kan juyin mulkin soji makusantan mutanen biyu ke ta kai gwaro su kai mari don ganin bangarorin biyu sun yi sulhu da ma dinke barakar da ta bayyana a tsakanin 'ya'yan jam'iyyar ta PNDS Tarayya wacce sojoji suka kifar da mulkinta. Dan siyasa Malam Alassan Intinikar da dan fafutika Soule Oumarou na daga cikin makusantan mutanen biyu da ke fatan ganin sun yi sulhu.

Sai dai Malam Assoumana Mahamadou mai kusanci da tsohon shugaban kasa Mahamadou Issoufou na ganin babu wata baraka a jam'iyyar balle a yi zancen sulhu.

Mohamed Bazoum yayin jawabi ga magoya baya
Mohamed Bazoum yayin jawabi ga magoya bayaHoto: Mohamed Bazoum

To amma Malam Chayib Mohamed wanda da ne ga hambararren shugaban kasa Mohamed Bazoum ya ce ko da za a kawo wani zancen sulhu, sai an cika sharadin sakin shugaba Bazoum da iyalinsa. Sai dai wasu masana ilimin diplomasiyya na ganin wannan baraka na iya haifar da wani sauyi a makomar jam'iyyar ta PNDS Tarayya.

Yanzu haka dai wasu daga cikin matasan jam'yyar ta PNDS Tarayya wadanda suke neman jagorancin jam'iyyar nan ba da jimawa ba, na nuna damuwa dangane da yadda rikicin manyan jam'iyyar ke barazana ga makomar jam'iyyar baki daya.