1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa za ta janye sojojinta daga Nijar

Salissou Boukari AH
September 25, 2023

Faransa ta sanar da matakin janye jakadanta da ma sojojinta daga Nijar, ayan da aka kwashe tsawon lokaci ana kai ruwa rana tsakanin gwamnatin Fransar da Nijar a kan batun.

https://p.dw.com/p/4Wm2I
Sojojin Faransa
Sojojin FaransaHoto: AP Photo/picture alliance

Lalle kaman yadda aka sani batu na farkoda ya haddasa babban cece-kuce a kasar ta Nijar shi ne sanarwar hukumomin kasar na mulkin soja da ta tabbatar cewa an hana tawagar kasar ta Nijar magana a zauran MDD bisa hadin bakin sakataran kungiyar da kuma Kasar Faransa, lamarin ya da ya harzuka 'yan Kasar ta Nijar. Za a iya cewa dai ganin yadda Faransa ta nace sai ta bai wa Nijar kunya a zauran taron na MDD ya sanya hukumomin mulkin sojin daga nasu bangare sake daukan matakin haramta wa duk wani jirgin kasar Faransa bi ta sararrin samaniyarta da ma jirgin wata kasa da 'yan Faransa ke cikisannan da jirgin soja wanda shi kuma sai da izini na musamman koma da yake ana haka kwatsam sai shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sanar da matakin janye jakadan kasar da ma sojojin na Faransa daga Nijar bayan da a baya ya yi kememe. Macron ya ce na samu tattaunawa da shugaba Bazoum, domin a wurinmu shi ne halastaccan shugaban kasa da al'umma ta zaba a Nijar kuma yake ci gaba da kasancewa a tsare, na ce mishi Faransa ta dauki aniyar janye jakadanta nan da 'yan awoyi masu zuwa tare da jami'an diflomasioyya namu da ke Nijar, sannan suma sojojin Faransa za su bar Nijar domin wannan hulda ta soja ta kare a tsakaninmu.

Emmanuel Macron
Emmanuel MacronHoto: Prime Minister's Office of Bangladesh/Handout/REUTERS

Sai dai kuma wata babbar magana da ta dauki hankali ita ce ta tsohon shugaban kasar ta Nijar Mahamadou Issoufou wanda ya ba ya goyon bayan a dauki matakin sojonjin kan Nijar, hakan ya jamnyo masa suka daga 'yan jam'iyyarsa da ke cewar shi ne ya kitsa juyin mulkin na Nijar da zumar saketsayawa takara a zaben shugaban kasar.