1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ambaliya ta yi sanadiyar rayukan mutane

Binta Aliyu Zurmi
October 22, 2022

Mamakon ruwan saman da ake tafkawa a jamhuriyar Nijar ya yi sanadiyar rayukan mutane sama da 190 yayin da ibtila'in ya haifar da babbar asara ga wasu da yawansu ya haura dubu dari uku.

https://p.dw.com/p/4IYdy
Nigeria Überschwemmung in Lokoja
Hoto: Ayodeji Oluwagbemiga/REUTERS

Ambaliyar da kasar ke fuskanta a wannan shekarar na zama mafi muni a tarihin kasar don ko a jiya Juma'a ma mutum 59 ne suka nutse a ruwa yayin da rushewar gidaje ta yi sanadiyar mutuwar mutum 136 wasu sama da 200 kuma sun sami munanan raunuka.

Yankunan jamhuriyar Nijar da ambaliyar ta fi yin barna sun hada da Maradi da Zinder da Dosso da jihar Tahoua.

Ko a shekarar da ta gabata ambaliya ta yi barna a kasar sai dai ta wannan shekarar ta yi tsananta kamar yadda sanarwar da mahukuntan kasar suka fidda ta bayyana.