1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Niger Delta sun koka kan rashin ci gaban yankin

January 9, 2019

Matasan na zanga-zangar a yankin Niger Delta kan abin da suka kira rashin tabuka abin kirki na hukumar ta NDDC da ke kula da raya yankin mai arzikin man fetur a Najeriya.

https://p.dw.com/p/3BHOs
Niger Kämpfer
Hoto: picture-alliance/dpa

Daruruwan Matasa da suka hada da 'yan bindiga sun fito daga Jahohi tara na yankin Niger Delta inda suka koka cewar, hukumar NDDC bisa Jagorancin Nsima Ekere ba ta tabuka komai ba dangane da ayyukan da suka kamata a rika yi wa yankin. 'Yan zanga-zangar da suka faro tun a ranar Litinin, sun ce za su ci gaba har sai hukumar ta NDDC da kuma fadar shugaban kasa sun ji kokensu.

Jagoran masu zanga-zangar Comrade Tonye Bobbo ya zargi shugabannin hukumar da yin danniya da kuma nuna wariya da Izgilanci. Ya ce wa’adin ‘yan hukumar gudanarwar NDDC  din ya kare tun shekarar da ta wuce wanda ya kamata a rush su a nada sabbi.

Nigeria Rebellengruppen legen Waffen nieder
Wasu matasa 'yan bindigar Niger DeltaHoto: picture alliance / dpa

Sakataren kungiyar ‘yan bindigar Niger Delta da aka yi wa afuwa, Kwamared Karo Edo, ya ce babu wani abin kirki da  hukumar ta NDDC ta yi a cikin shekaru uku karkashin jagorancin Nsima Ekere, don haka hukumar ta gaza, musamman ma wajen kulawa da matasan yankin. Matasan dai sun yi zargin cewa akwai ayyuka da dama da aka fara a baya, amma kuma aka yi watsi da su a garuruwan al'ummomin, alhali a garuruwan ake hako mai.