1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron EU da Turkiya kan 'yan gudun hijira

Mouhamadou Awal BalarabeMarch 7, 2016

Kasashen Turai na son hada gwiwa da Turkiya domin nemo mafita kan yadda 'yan gudun hijirar kasashen da ke Fama da yaki ke kwarara zuwa nahiyar Turai.

https://p.dw.com/p/1I8S4
EU Türkei Gipfel in Brüssel
Hoto: picture-alliance/dpa/O. Hoslet

Shugabannin kasashe da gwamnatocin Turai na gudanar da taron koli da takwaran aikinsu na Turkiya, da nufin gano dabarun katse wa 'yan gudun hijira hanyar shigowa Turai. Tuni ma shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi ganawar share fagen da takwaranta na Turkiya Ahmet Davutoglu domin ta nemi hadin kanshi wajen aiwatar da tsarin kasashen Turai.

Jaridar "Financial Times" ta ruwaito cewar kungiyar gamayyar Turai na son kafa wata cibiya da za ta kulla da miliyoyin 'yan gudun hijira da ke kwarara zuwa kasashen Turai. A taron koli na shugabannin EU da zai gudana a ranar 17 ga watan Maris ne za su yi nazarin wannan shawara. A yanzu dai duk kasar da ke zama mamba a kungiyar EU da ta fara karbar ‘yan gudun hijirar ce ke yi musu rejista tare da ba su mafaka idan bukatar hakan ta taso.