1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NATO na taro kan bai wa Ukraine makamai

May 31, 2024

Ministocin harkokin kasashen waje na kungiyar NATO, za su gana domin ci gaba da tattauna yadda za a tsara bai wa Ukraine makamai.

https://p.dw.com/p/4gTss
Kungiyar NATO na taro kan tallafin makamai ga Ukraine
Kungiyar NATO na taro kan tallafin makamai ga UkraineHoto: Petr David Josek/AP/picture alliance/dpa

A yayin zaman taron, ana sa ran ministoci su tattauna kan sanarwar Shugaba Joe Biden na Amirka, na bai wa Ukraine damar amfani da wasu makaman kasar kan Rasha. Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da yin kira kan a amincewa gwamnatin Kyiv, ta yi amfani da makaman da ake aikata mata wajen kai samame cikin Rasha.

Karin bayani: NATO za ta bai wa Ukraine karin makaman kakkabo jiragen yaki na sama

Sai dai akwai ayar tambaya da ake diga wa, kan wasu sharudda kasashe mambobin kungiyar NATO za su saka kan yadda Ukraine na amfani da makaman.

Babban sakataren kungiyar, Jens Stoltenberg ya ce akwai yiwuwar a dage wasu takunkumai na kai hari kan Rasha sakamakon yadda fada ke kara matsawa kusa da iyakar Ukraine. Sai dai gwamnatin Kremli ta ce a jira abun da zai biyo baya idan aka kaddamar da hari.