Najeriya: Zaman zullumi saboda rashin kammala zabe a wasu jihohi | Siyasa | DW | 14.03.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya: Zaman zullumi saboda rashin kammala zabe a wasu jihohi

Rashin kammala zaben gwamnoni a wasu jihohin Najeriya guda shida bayan zaben ranar 9 ga watan Maris ya janyo rashin tabbas da zaman dar-dar.

Ana cikin zaman zullumi sakamakon rashin kammaluwar zaben gwamnoni a wasu jihohi shida na Najeriya da suka hada da Kano, Sakkwato, Benue, Bauchi, Adamawa da Filato. Yanzu haka dai hukumar zaben kasar mai zaman kanta wato INEC ta sanya ranar 23 ga watan Maris zama ranar da za a gudanar da zabe a wadannan jihohi.

DW.COM