1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kama 'yan takara masu siyan kuri'a

March 9, 2019

Batun sayen kuri'u da magudi, sune suka mamaye zaben gwamnoni da na 'yan majalisar jiha da aka gudanar a wannan Asabar. Rahotannin na nuni da cewa, mutum 7 sun rasa rayukansu a sanadiyar hatsaniyar ranar zaben.

https://p.dw.com/p/3Ehbc
Wahlen in Nigeria
Hoto: AP

A jahar Ebonyi ma dai, an cinna wa rumfunan zabe akalla uku wuta, inda kayyakin da hukumar zaben ta ajiye suka kone kurmus. Haka lamarin ya ke a jahar Benuwe da ke tsakiyar Najeriyan.

Masu sa ido kan zaben Najeriyan kuwa, sun ce sun ga wuraren da aka yi ta kwace akwatunan zabe, yayin da hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC a shafinta na twitter, ta wallafa labarin kame buhuhunan kudi da aka fito da su domin siyan kuri'u, baya ga haka ta ce ta kama wani dan takara majalisar wakilai na jahar Ogun da fiye da naira miliyan daya da ya kakkasa a cikin wani buhu. 

Kafar yada labaran AP kuwa,  ta sheda ganin yadda aka yi ta siyan kuri'u akan Naira dubu daya a jahar Delta. Jihohi ashirin da tara aka gudanar da zaben gwamnonin daga cikin talatin da shida da ake da su a kasar.

Gwamnonin Najeriya dai na da karfi a siyasar kasar musamman tasirinsu ga gwamnatin tarayya, inda suke kuma da karfi a muhimman fannonin da suka hada da ilimi da kuma lafiya.