Bauchi: ′Yan sanda sun tarwatsa wakilan ′yan siyasa a INEC | Labarai | DW | 10.03.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bauchi: 'Yan sanda sun tarwatsa wakilan 'yan siyasa a INEC

Fada ya barke tsakanin jami'an tsaro da wasu wakilan jam'iyyun siyasa a cibiyar hukumar zabe ta INEC a Jihar Bauchi inda jami'an tsaron suka lakkada musu duka. 

Rikicin ya taso ne sakamakon gaza bayyana sakamakon zaben karamar hukumar Tafawa Balewa da shugabar zaben jihar ta gaza yi a karo na biyu. Wannan lamari shi ya haddasa wakilan jam'iyyun suka nuna rashin amincewa da matakin da suke ganin akwai rufa-rufa a ciki.